logo

HAUSA

Xi ya bukaci Jamus da EU da su hada kai da Sin don kara samar da tabbaci da kwanciyar hankali a duniya

2021-04-07 20:15:37 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci kasar Jamus da kungiyar tarayyar Turai (EU), da su hada kai da kasar Sin, don kiyaye tare da bunkasa dauwamammen hadin gwiwa mai tsafta, a wani mataki na kara samar da tabbaci da kwanciyar hankali a duniya dake fama da tashin hankali.

Xi wanda ya yi wannan kira Larabar nan yayin zantawa ta wayar tarho da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ya ce ci gaban kasar Sin wata dama ce ga kungiyar tarayyar Turai(EU), don haka ya bukaci EUn da ta yanke hukuncin da ya dace ba tare wani ya tsoma mata baki ba, ta yadda za ta ci gajiyar ‘yancin da take da shi. (Ibrahim)

Ibrahim