logo

HAUSA

Shirin kasar Sin ya lashe kyautar fasahar zamani ta UNESCO

2021-04-07 11:47:44 CRI

Shirin kasar Sin ya lashe kyautar fasahar zamani ta UNESCO_fororder_210407-dalibin jami'a

Wani shiri mai taken, “Dalibi guda a kowanne kauye” wanda jami’ar koyo daga gida wato Open University of China ta bullo da shi, ya yi nasarar lashe kyautar ilmin fasahar zamani ta ICT ta hukumar raya ilmin kimiyya da al’adu ta MDD wato UNESCO na shekarar 2020.

Hukumar ta UNESCO wanda ke da babban ofishinta a birnin Paris, ta sanar da hakan a jiya Talata.

Shirin wanda aka kaddamar da shi a shekarar 2004 domin cike gibin da ake da shi a fannin ilmin gaba da sakandare da kuma koma bayan bunkasar tattalin arzikin da ake fuskanta a kauyuka da yankunan karkarar kasar Sin, shirin ya yi amfani da fasahar kwaikwayon tunanin bil adama wato AI wajen samarwa dalibai daga yankunan karkara damammakin samun ingantattaun kayayyakin koyon karatu.

A cewar hukumar ta UNESCO, shirin ba kawai ya inganta makarantun yankunan karkarar da kuma bullo da shirye shiryen koyar da ilmi na dogon zango ba ne, har ma ya inganta amfani da fasahohin AI da VR, wadanda suke da matukar tasiri wajen baiwa dalibai kwarewa da ba su kwarin gwiwa.

Shirin na kasar Sin yana aiki ne ta hanyar tsarin koyarwa ta zamani wanda ya kunshi amfani da sautin muryoyi da bayanan na’ura mai kwakwalwa, da aikewa da sakonnin nan take, da kuma yadda ake sarrafa manyan bayanai ta hanyar na’urorin zamani. Ya zuwa shekarar 2020, sama da dalibai dubu 800 ne suka amfana da shirin a duk fadin kasar. (Ahmad)