logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya nada mukaddashin sefiton ’yan sandan kasar

2021-04-07 09:58:39 CRI

Shugaban Najeriya ya nada mukaddashin sefiton ’yan sandan kasar_fororder_210407-yan sanda

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nada mai rikon mukamin sifeton ’yan sandan Najeriya domin tsara dabarun tinkarar matsalolin tsaron kasar, da nufin kawo karshen kalubalolin tsaron dake damun kasar ta yammacin Afrika.

Ministan al’amurran ’yan sandan Najeriya, Maigari Dingyadi, ya bayyanawa ’yan jaridu a Abuja cewa, an nada Usman Baba a matsayin mai rikon mukamin sifeton ’yan sandan kasar, kuma nadin nasa ya fara aiki ne nan take.

Baba zai karbi ragamar aiki daga hannun Mohammed Abubakar Adamu, wanda shugaban kasa ya tsawaita wa’adin aikinsa da watanni uku a ranar 4 ga watan Fabrairu. (Ahmad)