logo

HAUSA

Sifeton ’yan sandan Najeriya ya bukaci a kara sanya ido bayan wani hari a kudancin kasar

2021-04-07 09:34:47 CRI

Sifeton ’yan sandan Najeriya ya bukaci a kara sanya ido bayan wani hari a kudancin kasar_fororder_210407-Owerri

A jiya Talata babban sifeton ’yan sandan Najeriya ya bukaci jami’an ’yan sandan kasar da kuma al’umma da su zauna cikin shiri kana su kara sanya ido yayin da aka samu hare hare da aka kaddamar a helkwatar ’yan sanda da gidan yarin jahar Imo dake kudancin kasar a ranar Litinin.

Mohammed Abubakar Adamu, babban sifeton ’yan sandan Najeriyar, ya yi wannan kira ne a Owerri, babban birnin jahar Imo, yayin da ya ziyarci helkwatar ’yan sandan, ya kara da cewa, an tura karin dakaru na musamman zuwa jahar domin dakile ayyukan ’yan bindigar.

Ya kuma gargadi jami’an ’yan sandan jahar da cewa kada su yi kasa a gwiwa a yaki da ’yan fashi, sannan ya jaddada cewa, ba za su taba yin sulhu da bata-gari ba.

Wasu ’yan bindiga da ba a san su ba sun kaddamar da hari a helkwatar ’yan sanda da gidan yari a birnin Owerri a safiyar ranar Litinin, inda suka saki mazauna gidan yarin sama da 1,800 da ake tsare da su, kamar yadda hukumomin ’yan sandan suka bayyana. (Ahmad Fagam)