logo

HAUSA

Ya zama wajibi a wanzar da nasarar tsarin siyasa a Mali in ji jakadan kasar Sin

2021-04-07 09:58:54 CRI

Ya zama wajibi a wanzar da nasarar tsarin siyasa a Mali in ji jakadan kasar Sin_fororder_daibing

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya bayyanawa zaman kwamitin tsaron majalissar cewa, ya zama wajibi a wanzar da nasarar tsarin siyasa a kasar Mali.

Dai Bing wanda ya yi wannan tsokaci a jiya Talata, ya ce daukacin yanayin siyasa a Mali yana kara kyautata, a lokaci guda kuma kasar na fuskantar kalubalen ta’addanci, da bazuwar cutar COVID-19, da kuma matsalolin jin kai. Don haka ya dace sassan kasa da kasa su mai da hankali wajen baiwa Mali dukkanin tallafin da ya wajaba.

Jami’in ya ce gwamnatin Mali ta tsara shirin mika mulki ga zababbiyar gwamnati, kuma aiwatar da hakan shi ne mataki na gaba.

Dai Bing ya kara da cewa, gwamnatin kasar na aiki tukuru wajen tsarawa, da fadada shirye shiryen zabubbuka, amma duk da haka akwai bukatar kara kaimi don bunkasa wannan ci gaba, da kara inganta rayuwar al’umma, ta yadda hakan zai haifar da karin gajiya ga al’ummun kasar.  (Saminu)

Saminu