logo

HAUSA

Najeriya ta sanya wuraren gyaran hali cikin shirin ko-ta-kwana

2021-04-07 19:39:51 CRI

Rahotanni daga Najeriya na cewa, an tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin gyaran hali dake fadin kasar, biyo bayan harin da wasu bata gari suka kai a ranar Litinin kan hedkwatar ‘yan sanda da gidan yari a jihar Imo dake yankin kudancin kasar.

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, shi ne ya bayyana haka, yayin ziyarar da ya kai cibiyar gyaran hali dake garin Owerri na jihar Imo, don duba irin barnar da ‘yan bindiga suka yi bayan harin da suka kai cibiyar. Ya kuma ba da tabbacin cewa, za a kara tsaurara matakan tsaron kasar, har ma a dukkan cibiyoyin gyaran hali dake sassan daban-daban na kasar.

Ya kuma yi Allah wadai da harin, inda ya ba da tabbacin cewa, za a gano tare da hukunta wadanda suka aikata wannan danye aiki.

A don haka, Osinbajo ya bukaci hukumomin tsaro, da kada su yi kasa a gwiwa a yakin da ake yi da ‘yan bindiga, duk da kalubalen da ke tattare da wannan aiki.(Ibrahim)

Ibrahim