logo

HAUSA

Wang Yi: Sin da ASEAN suna adawa da mallake alluran riga kafi

2021-04-07 21:23:34 CRI

Jaridar nan ta kasar Singapore mai suna Lianhe Zaobao, ta ruwaito ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi yana jaddada cewa, kasarsa ba ta gindaya wani sharadi na diplomasiyya a fannin alluran riga kafi ba. Yana mai cewa, kasarsa za ta tattauna da kasar Singapore, kan yadda za a bunkasa alaka a fannin samarwa, adanawa, da kuma jigilar alluran riga kafin COVID-19.

A ranar 31 ga watan Maris zuwa 3 ga watan Afrilu ne, Wang Yi ya gana da ministocin harkokin wajen kasashen Singapore, da Malaysia, da Indonesia da Philippines da Koriya ta Kudu a lardin Fujian.

Wang Yi ya ruwaito wani minsitan harkokin waje daga kasashen ASEAN na cewa, kasar Sin ba ta gindaya wani sharadi na diplomasiyya a fannin alluran riga kafi ba, tana nuna nauyin dake bisa wuyanta a matsayinta na babbar kasa.

Wany Yi ya bayyana cewa, kasashe masu wadata, wadanda ke da kaso 16 cikin 100 na yawan al’ummar duniya, sun mallaki kaso 60 cikin 100 na alluran riga kafin da ake samarwa a duniya, inda ya bayyana yanayin a matsayin abin takaici. (Ibrahim)

Ibrahim