logo

HAUSA

MDD: COVID-19 ta bankado yanayin rashin daidaito tsakanin al’ummun duniya

2021-04-06 10:59:41 CRI

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya ce cutar COVID-19, ta bankado yanayin rashin daidaito tsakanin al’ummun duniya. Mr. Guterres wanda ya bayyana hakan cikin wani sako da ya fitar, albarkacin ranar lafiya ta duniya dake tafe a ranar Laraba, ya ce rashin daidaito da adalci, sun kara bayyana a fili sakamakon bullar wannan annoba.

Ya ce mafi yawan alluran rigakafin wannan cuta sun kasance ne a hannun kasashe mawadata, ko wuraren da ake sarrafa su domin rarrabawa. Kuma a cikin kasashen ma, rashin lafiya da rashe rashe sakamakon harbuwa da COVID-19, sun fi yawa ne tsakanin al’ummun dake fuskantar talauci, da masu aiki ko rayuwa cikin mawuyacin hali, ko wadanda suke fuskantar wariya ko tsangwama.

To sai dai kuma a cewar jami’in, shirin COVAX na MDD ya kasance wani muhimmin yunkuri na kasa da kasa, wanda ya samar da daidaito a fannin rabon rigakafin, ta yadda karin kasashe ke samun sa, ko da yake har yanzu, ga kasashe masu karanci da matsakaicin kudaden shiga, ba su da abun yi sai jira.  (Saminu)