logo

HAUSA

Masanin Najeriya: Inganta tsarin zabe na Hong Kong da aka yi, ya yi daidai kuma yana da ma’ana kwarai

2021-04-06 12:35:07 cri

Masanin Najeriya: Inganta tsarin zabe na Hong Kong da aka yi, ya yi daidai kuma yana da ma’ana kwarai_fororder_微信图片_20210406095806

Kwanan baya, Shehun malami a kwalejin nazarin harkokin siyasa da huldar kasa da kasa a jami’ar Abuja dake tarayyar Najeriya Agaba Halidu, ya rubuta wani sharhi, game da ingancin tsarin zabe na Hong Kong a jaridar Blueprint, inda ya bayyana cewa, Hong Kong ya kasance wani yanki da ba za a iya raba shi daga yankin kasar Sin ba tun fil azal, kuma kwanan nan, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta inganta tsarin zaben Hong Kong, wanda hakan ya yi amfani a fannin kiyaye wadata da zaman karko na dogon lokaci a yankin, kana ya ba da tabbaci wajen aiwatar da manufar “Kasa daya amma tsari iri biyu” yadda ya kamata a yankin.

Sharhin ya ce, bayan da aka maido da Hong Kong a karkashin mulkin kasar Sin a shekarar 1997, ya zama yanki na musamman mai bin manufar "Kasa daya amma tsari iri biyu". Kaza lika inganta tsarin zabe a yankin musamman na Hong Kong na da mahimmancin gaske, domin zai tabbatar da aiwatar da manufar "masu kishin kasa su yi mulkin Hong Kong".

Fadada kwamitin zaben, babu shakka zai taimaka wajen kara shigar da mazauna yankin na Hong Kong a harkokin siyasa, da karfafa hadin kan muradun yankin da bukatun kasa, ta yadda za a kare babbar moriyar mazauna yankin.

Ya ce inganta tsarin zaben na Hong Kong, mataki ne da ya dace kwarai, wanda ba wai kawai zai ba da damar mutunta hakkokin dimokuradiyya na jama'a ba ne, har ma zai taimaka ga kiyaye mulkin kan kasa, da tsaro, da muradun ci gaban kasar yadda ya kamata. (Bilkisu)