logo

HAUSA

Xi ya aika sakon ta’aziya ga takwaransa na Indonesiya dangane da bala’in da ya aukawa kasar

2021-04-06 19:45:33 CRI

Xi ya aika sakon ta’aziya ga takwaransa na Indonesiya dangane da bala’in da ya aukawa kasar_fororder_1127295060_16176041908591n

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikawa takwaransa na kasar Indonesiya Joko Widodo sakon ta’aziya, dangane da ambaliyar ruwa da zaftarewar laka da ka faru a yankin kudu maso gabashin kasar dake yankin Asiya.

A cikin sakon nasa, Xi ya bayyana cewa, ya kadu da samun labarin ambaliyar ruwa da zaftarewa lakar da ta haddasa hasarar rayuka.

Shugaba Xi ya ce, a madadin gwamnatin kasar Sin da al’ummarta da ma shi kansa, yana mika ta’aziya kan wadanda lamarin ya shafa, tare da jajantawa iyalan wadanda suka ji rauni.(Ibrahim)

Ibrahim