logo

HAUSA

Ministan Wajen Sin Ya Bukaci Amurka Da Ta Mutunta Muhimman Muradun Sin

2021-04-05 16:25:39 CRI

Ministan Wajen Sin Ya Bukaci Amurka Da Ta Mutunta Muhimman Muradun Sin_fororder_sin

Dan majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bukaci kasar Amurka da ta mutunta muhimman muradun kasar Sin ta kuma kalli ci gaban kasar ta hanyar da ta dace.

Wang ya bayyana haka ne, lokacin da yake amsa tambayar da manema labarai suka yi masa, game da alakar Sin da Amurka, bayan ganawa da takwarorinsa na kasashen Singapore, da Malaysia, da Indonesia, da Philippines, da Korea ta Kudu a lardin Fujian na kasar Sin.

Jami’in na kasar Sin ya bayyana cewa, ministocin wajen kasashen, suna daukar bunkasuwar kasar Sin a matsayin abin da tarihi ba zai manta da shi ba. Ya kuma yi imanin cewa, bunkasuwar kasar Sin, ta yi daidai da abin da kasashen ke tsammani da ma muradun dogon zango na dukkan kasashen dake shiyyar, wadanda bai dace a dakatar da su ba.

Da ya juya ga batun kace na kace kan batun takara, da hadin gwiwa da yin fito na fito da Amurka ta sha nanatawa game da hadin gwiwarta da kasar Sin, Wang ya ce, matsayin kasar Sin a fili yake kuma bai sauya ba.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana maraba da yin tattaunawa ta hanyar nuna daidaito da mutunta juna. Kasar Sin tana adawa da wata kasa daya ta yi mulkin duniya, ba kuma za ta amince kasa daya ta kasance sai abin da fada kowa zai bi ba.

Wang Yi ya ce, kasarsa tana maraba da yin hadin gwiwa, idan bukatar hakan ta taso, amma hadin gwiwar ta yi la’akari da damuwan juna da cin moriyar juna. Ba wai hadin gwiwar da bangare daya zai rika gindaya sharadi da zayyawa jerin wasu abubuwa ba. (Ibrahim)

Ibrahim