logo

HAUSA

Denja Abdullahi: Dan Najeriya dake kokarin fassara littattafan kasar Sin daga harshen Turanci zuwa Hausa

2021-03-30 16:33:46 CRI

Denja Abdullahi: Dan Najeriya dake kokarin fassara littattafan kasar Sin daga harshen Turanci zuwa Hausa(A)_fororder_微信图片_20210330163222

Malam Denja Abdullahi, shugaban asusun kula da harkokin rubuce-rubuce mai suna Orpheus Literary Foundation dake Najeriya, kana darektan hukumar fasaha da al’adu ta kasar reshen jihar Bauchi, wanda kuma shi ne tsohon shugaban kungiyar marubutan Najeriya baki daya ko kuma ANA a takaice.

A zantawar sa da Murtala Zhang, malam Denja Abdullahi ya bayyana tarihinsa, gami da jajircewar da shi gami da ma’aikatansa suke yi na fassara wasu littattafan kasar Sin biyar daga yaren Turanci zuwa Hausa tun daga shekara ta 2016. Ya kuma bayyana yadda suka gudanar da ayyukan fassara gami da ma’anar fassara littattafan Sin zuwa harshen Hausa, wanda shi ne daya daga cikin manyan harsuna a yankunan yammacin Afirka.(Murtala Zhang)