logo

HAUSA

Wang Yi: Mahangar kasashen yamma kan batun hakkin dan-Adam bai wakilci dukkan kasashen duniya ba

2021-03-29 09:35:38 CRI

Dan majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana cewa, ra’ayoyin kasashen yammacin duniya game da batun hakkin dan-Adam, ko kadan bai yi dai-dai da na kasashen duniya ba.

Wang Yi wanda ke ziyara a hadaddiyar daular kasashen Larabawa(UAE), ya bayyana haka ne, yayin ganawa da takwaransa na kasar Sheikh Abdullah bin Zayed al-Nahyan a Abu Dhai, fadar mulkin kasar.

Ministan ya ce, al’ummomin kasashe ne, za su yi alkalanci game da yanayin hakkin dan-Adam na kasashensu, maimakon ra’ayoyin wasu kasashe. Yana mai cewa, ya kamata duniya ta saurara ta kuma fahimci ra’ayoyin kasashe masu tasowa, ta yadda ma’anar hakkin dan-Adam da za ta zama cikakkiya, mai kunshe da dukkan fannoni da kuma daidaito.

Wang Yi ya jaddada cewa, ‘yancin rayuwa da samun ci gaba, suna da muhimmanci kamar ‘yancin na siyasa da jin dadin rayuwa, sannan ya kamata a martaba gaskiya da adalci, kamar yadda ake martaba tsarin demokuradiya da ‘yanci.(Ibrahim)