logo

HAUSA

Za a gudanar da taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS

2021-03-23 11:17:59 CRI

A yau da safe, kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin, ya gudanar da taron manema labaru, inda ya yi bayani game da shirya gudanar da taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS.

Mataimakin ministan kula da ayyukan fadakarwa na yau da kullum, na kwamitin tsakiya na JKS Wang Xiaohui ya bayyana cewa, kwamitin tsakiyar zai gudanar da taron murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS, inda babban sakataren kwamitin tsakiya, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping zai bada muhimmin jawabi.

Kana kwamitin tsakiya na JKS zai bada lambobin yabo ga wasu membobin jam’iyyar da suka fi samar da gudummawa ga jam’iyyar. A hannu guda kuma, shugaba Xi Jinping zai ba su takardu da lambobin yabo. (Zainab)