logo

HAUSA

Ziyara zuwa titin shagunan sayar da kofin kasashen Afirka a kasar Sin

2021-03-19 17:10:59 CRI

Kofi na daya daga cikin manyan abubuwan sha guda uku na duniya, wato baya ga koko da kuma shayi, wanda ya samu karbuwa sosai a kasashen duniya. Amma a hakika, kofi ya samo asalinsa ne a nahiyar Afirka, wato a yankin plato da ke kudu maso yammacin kasar. An ce, yau kimanin shekaru dubu da suka wuce, wani makiyayi ne ya gano bishiyar kofi, bayan da akuyarsa ta ci ganyen, sai kuma ta samu kuzari sosai. Sai dai wasu na cewa, mazauna yankin sun gano bishiyar kofi ne bayan da aka samu tashin gobara a dajin bishiyoyin kofi, kuma kamshin da bishiyoyin suka fitar bayan da suka kama wuta ya jawo hankalin mazauna dake kewayen.

Ziyara zuwa titin shagunan sayar da kofin kasashen Afirka a kasar Sin_fororder_微信图片_20210319170556

Duk da cewa babu tabbaci game da yadda aka gano bishiyoyin kofi har aka fara hada abin sha da shi, amma muna iya tabbatar da cewa, kofi ya samo asalinsa ne a nahiyar Afirka, kuma daga bisani an yayata shi zuwa sassan duniya. Baya ga haka, har yanzu kofi da kasashen Afirka suka fitar, musamman ma Habasha da Kenya da sauransu, sun shahara a duniya a sakamakon ingancinsu.

A nan kasar Sin ma, kofi na kara samun karbuwa a cikin ‘yan shekarun baya. Har ma a bara, a birnin Changsha, hedkwatar lardin Hunan da ke tsakiyar kasar Sin, an kaddamar da wani titi na sayar da kofi na Afirka.

Kasancewar titin dake kasuwar Gaoqiao ta birnin Changsha, da shigar mu titi, sai mu ka ji kamshin kofi yana fitowa daga kantuna da ke gefunan titin.

Ziyara zuwa titin shagunan sayar da kofin kasashen Afirka a kasar Sin_fororder_微信图片_20210319170606

Fadin titin ya kai muraba’in mita sama da 5000, inda aka hada kamfanonin sai da kofi fiye da 20 a gu daya, wadanda suke sayar da kofi da aka shigo da su daga Habasha da Kenya da Rwanda da Tanzania da ma sauran kasashen Afirka, kuma Glory Coffee na daya daga cikin kamfanonin.

Malam Li Ruikai, babban darektan kamfanin Glory Coffee, ya ce, a yayin da mu’amalar ciniki da tattalin arziki ke kara karfafa, a watan Yunin shekarar 2019, an kaddamar da bikin baje kolin harkokin tattalin arziki da cinikayya karo na farko a birnin Changsha, hedkwatar lardin Hunan. Bayan da aka kammala bikin kuma, an tsara shirin “kaddamar da bikin baje kolin harkokin tattalin arziki da cinikayya da babu iyaka” a kasuwar Gaoqiao, inda aka hada kan wasu kamfanonin sayar da kofi 20 don su kaddamar da wannan titi na sayar da kofi na Afirka. Titin da ya kasance na farko a kasar Sin da ke sayar da kofi na kasashen Afirka. Malam Li Ruikai ya kara da cewa,“Jigon wannan titi a bayyane ya ke, wato yanzu kamfanonin da ke titin na mai da hankali a kan tallata kofi na kasashen Afirka, sabo da kun san ban da Afirka, kasashen tsakiyar Amurka da kuma kudu maso gabashin Asiya ma suna samar da kofi. Da ma kofi na Afirka na samun karbuwa sosai a wurinmu, musamman ma kofi nau’in Yirgacheffe da kasar Habasha ke fitarwa da kuma kofi na Kenya, dukkansu na da kyau sosai. Muna kuma fatan ta bikin baje kolin harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka da aka shirya a birnin Changsha, za a kara shigowa da waken kofi na kasashen Afirka zuwa nan kasar Sin. Wannan shi ne burin kowane kamfani da ke wannan titin.”

Ziyara zuwa titin shagunan sayar da kofin kasashen Afirka a kasar Sin_fororder_微信图片_20210319170630

Idan mutum ya shiga kantin kamfanin Glory Coffee da ke titin, zai ga waken kofi iri iri na kasashen Habasha da Kenya da Rwanda da aka jera su, baya ga kuma nau’o’in na’urori na sarrafa kofi da aka samar a kasashe daban daban. Abin lura shi ne, a cikin kantin, akwai kuma cibiyar horar da dabarun hada kofi. A game da wannan, malam Li Ruikai ya ce, ban da sayar da waken kofi, kamfaninsa yana kuma samar da hidimomin da suka shafi kofi, yana mai cewa,“Tsarin mu shi ne, idan mutum yana son bude gidan shan kofi, kuma ya zo wajenmu, to, za mu nuna masa hidimomin da suka shafi zabar wurin gudanar da gidan shan kofi da tsara fasalinsa, misali da farko za a tabbatar da wurin, ko ya kasance a titin kasuwanci ne ko a jami’a ce, ko kuma a ginin ofisoshi ne, kuma bisa ga wurin da aka tabbatar, za mu tsara fasalin gidan mabambanta. Baya ga haka, za mu kuma horar da ma’aikatansa. Wato ba lalle ne a samu kwarewa a fanni ba, kawai in dai ana da niyyar bude shi, za mu yi masa kome da kome.”

Ziyara zuwa titin shagunan sayar da kofin kasashen Afirka a kasar Sin_fororder_微信图片_20210319170625

Malam Li Ruikai ya ce, dalilin da ya sa yake dukufa kan tallata kofi na Afirka tare da gudanar da harkokin da suka shafi kofi shi ne, sabo da ya ga makomar kasuwar kofi a kasar Sin. Ya ce,“Da a yayin da nake hira da abokaina, na kan ce musu, sana’ar kofi za ta kiyaye bunkasuwar da ta kai sama da kaso 10% a kowace shekara nan da shekaru 50 masu zuwa. Amma yadda gidan shan kofi na Luckin Coffee ya samu matukar nasara a kasar, ya kara raya sana’ar kwarai da gaske, akwai babbar kasuwa. Don haka nake gudanar da cibiyar horar da ayyukan hada kofi, kuma ina da imani sosai ga makomar sana’ar a kasar.”(Lubabatu)