logo

HAUSA

Karin kasashe na goyon bayan matakan kasar Sin na kare hakkin bil-Adama

2021-03-17 09:00:00 CRI

A yayin da ake ci gaba da taron hukumar kare hakkin bil-Adama na MDD karo na 46, kasar Sin na kara samun goyon bayan kasashe, kan yadda take kare hakkin bil-Adam a yankunan Xinjiang da Tibet, duk da yadda wasu kasashen yamma ke fakewa da wannan batu suna tsoma baki a wadannan yankuna na kasar Sin, wanda hakan tamkar tsoma baki ne a harkokin cikin gidan na kasar Sin.

Karin kasashe na goyon bayan matakan kasar Sin na kare hakkin bil-Adama_fororder_20210317世界21009-hoto1

Na baya-bayan shi ne, wanda kasar Cuba ta gabatar da wata sanarwar hadin gwiwa a madadin kasashe 64, inda ta bukaci dukkan sassa, da su yayata tare da kare hakkin bil-Adam ta hanyar tattaunawa mai ma’ana, kana su nuna adawa da yadda ake siyasantar da batutuwan da suka shafi kare hakkin bil-Adam, da yadda suke nuna fuska biyu.

Kasashen sun kuma yaba da tsarin gwamnatin kasar Sin na nacewa kan mayar da jama’a a gaban komai, da irin nasarorin da kasar ta cimma a fannin kare hakkin bil-Adam. Kasashen sun kuma jaddada cewa, Xinjiang, wani yanki ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba, don haka, kamata ya yi a daina amfani da batutuwan da suka shafi yankin na Xinjiang, don tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, da daina zargin kasar Sin babu gaira babu dalili saboda batu na siyasa, da daina duk wasu ayyuka da za su hana ci gaban kasashe masu tasowa ta hanyar fakewa da batutuwan kare hakkin bil-Adama.

A wannan rana, wasu kasashe masu tasowa irinsu Sri Lanka, da Koriya ta Arewa, da Sudan ta kudu, da Kamaru, da Azerbaijan da Kwadebuwa, su ma sun bayyana goyon bayansu ga kasar Sin kan batutuwan da suka shafi Yankunan Xinjiang da Hong Kong.

Karin kasashe na goyon bayan matakan kasar Sin na kare hakkin bil-Adama_fororder_20210317世界21009-hoto2

A jawabin da ya gabatar a madadin kasashen dake da irin wannan ra’ayi, zaunannen wakilin kasar Sin dake ofishin MDD dake Geneva da sauran hukumomin kasa da kasa, Chen Xu ya jaddada bukatar tattaunawa mai ma’ana da yin hadin gwiwa a fannin kare hakkin bil-Adama, ya kuma nuna adawa da yadda wasu kasashe suke siyasantar da batutuwan da suka shafi wannan batu da ma nuna fuska biyu.

Ya ce, saboda batutuwa na siyasa, kasashen da abin ya shafa, sun sha zargin kasashe masu tasowa tare da tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe, wanda hakan ya keta dalili da ma ka’idojin da suka kai ga kafa MDD.

A don haka, ya bukaci kasashen da abin ya shafa, da su martaba kalamai da abubuwan da suke aikatawa, su tashi tsaye su magance batutuwan kare hakkin bil-Adama dake damunsu, su kuma yi kokarin hada kai da sauran kasashen duniya a fannin kare hakkin bil-Adam. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)