logo

HAUSA

Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim: Jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin babban dalili ne na ci gaban kasar(A)

2021-03-16 14:33:58 CRI

Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim: Jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin babban dalili ne na ci gaban kasar_fororder_rBABCWBG7eKAfUtBAAAAAAAAAAA834_912x436_801x383

Bana jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin take cika shekaru 100 da kafuwa, inda Murtala Zhang ya samu damar zantawa da Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, darektan cibiyar horas da ‘yan majalisu na jami’ar Abuja, wanda kuma shi ne shahararren masanin harkokin kasar Sin a tarayyar Najeriya.

Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim ya yi tsokaci kan muhimmiyar rawar da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta taka tun kafuwarta har zuwa yanzu, wato yadda ta jagoranci al’ummar kasar wajen gwagwarmayar kwato ‘yanci, da zama jam’iyya mai mulki a kasar, ta kuma jagoranci aikin samar da ci gaba a fannoni da dama a kasar ta Sin.

Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim ya kuma ce, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ba kawai ta bayar da gudummawa mai yawa ga ci gaban kasar ba ne, har ma ta zama tamkar abun misali ga duk duniya, ganin yanayin kwazo da jajircewarta a fannin samar da ci gaba da kawo alheri ga al’ummomi daban-daban.(Murtala Zhang)