logo

HAUSA

Mahinur Abdullah: Taimakawa wasu da kuma kara kyautata halin da nake ciki

2021-03-16 10:40:21 cri

Mahinur Abdullah: Taimakawa wasu da kuma kara kyautata halin da nake ciki_fororder_马伊努尔

Yanzu dai, ba kawai Sinawa masu aikin sa kai suna taka rawarsu a fannoni daban daban a cikin kasar ba, har ma su kan yi tattaki zuwa kasashen waje don taimakawa ‘yan uwa dake waje. Wadannan Sinawa ana kiransu masu aikin sa kai ta fuskar ba da taimako ga ofishin jakadanci. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku labarin Mahinur Abdullah, wadda ke aikin sa kai a ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Turkiya.

A shekarar 2013, kamfanin da Mahinur Abdullah ta ke aiki, ya tura ta zuwa birnin Antalya na kasar Turkiya, domin zama babbar daraktar sashen kamfanin dake wurin. Saboda ta kware sosai a harshen Turkanci, ta kan taimaka wa ofishin jakadancin da ke Turkiya don kula da wasu lamuran da ke faruwa a can. Don haka, lokacin da Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar Sin ta fara gudanar da ayyukan tsara masu aikin sa kai a fannin ba da taimako ga ofisoshin jakadancin kasar, sai ofishin jakadancin Sin da ke Turkiyya ya yi tunani kan Mahinur Abdullah.

Mahinur ta ce, tun da Antalya sanannen birni ne a fannin yawon bude ido a kasar Turkiyya, galibin ayyukan taimako da ofishin jakadancin yake samu, sun shafi masu yawon bude ido ne. Da take bayani game da abin da ba za ta taba mantawa da shi ba, Mahinur ta ce,

"Dalilin da ya sa ba zan manta ba shi ne, na tsora lokacin da wasu iyalai su hudu, su ka yi hayar wata mota, amma motar ta kife a kan hanya. Sun shiga damuwa sai su ka buga waya ofishin jakadancin domin neman tallafi. A lokacin, ofishin Jakadancin ya kira ni a tsakiyar dare, suka fada min, lamarin ya faru ne a wani wurin mai wahalar shiga.”

Mahinur ta ce, an yi sa'a, babu wanda ya ji rauni. Nan da nan ta tuntubi kamfanin motocin da suka yi haya da kuma 'yan sanda don ceto da magance hadarin da ya rutsa da su, kana ta taimaka wa wadannan masu bude ido don zuwa wani wuri mai tsaro a kan lokaci. Tun da aka magance lamarin cikin awoyi 2 kacal, hakan bai shafi wurin da iyalin za su tafi ba. Saboda haka, a yayin da suka bar Antalya, sun yi ta nuna godiyarsu ga Mahinur.

A shekarar 2020, an samu bullar annobar numfashi ta COVID-19 ba zato ba tsamani, lamarin da ya sa Mahinur ta kara fahimtar ayyukanta na taimakawa ofishin jakadanci, wato karfin saurara da sanyaya zuciya na da muhimmanci sosai.

Wasu tsoffin ma'aurata 'yan kasar Sin da ke aiki a wani otel da ke karkarar Antalya. Inda matar ta kamu da annobar COVID-19, saboda ba su iya yaren wurin ba, ba su iya yin mu’amala sosai tare da masu aikin jinya ba, don haka ba su gamsu ba kuma sun damu sosai kan jinyar da asibitin wurin ya baiwa matar. Don haka, sun nemi taimako daga ofishin jakadancin. Bayan da ofishin jakadanci ya buga mata waya, Mahinur ta tuntubi otal din da asibitin a kan lokaci, don taimaka mu su sake zuwa asibiti, domin samun jinya, inda ta zama gadar yin cudanya a tsakanin marasa lafiya ciwon da likita. Kana ta yi kokarin sanyaya zuciyar dangogin tsoffin biyu dake kasar Sin. Bisa kokarin da ta yi, halin tsohuwar data kamu da cutar ya kyautatu.

Mahinur ta ce, yayin da suke fuskantar mutuwa, suna taka rawa a matsayin wani ginshiki na masu neman taimako a fannin tunani.

“A hakika dai, a yawancin lokuta, suna dauka ta a matsayin mai kwantar da hankali. Kamar yadda aka sani, idan an ambaci yaduwar COVID-19, jama’a na nuna damuwa sosai, kuma idan babu dangogi ko abokan da za su raka su, to damuwar da suke ciki za ta kara tsananta.”

Ko da yake irin wadannan ayyukan sa kai, sun sanya Mahinurkara tana fama da aiki, duk da haka, tana samun lokaci don yin wasu abubuwa daidai gwargwadon karfinta don taimaka wa Sinawa dake gamuwa da matsaloli a wurin. Ta hanyar gudanar da ayyukan, ta sami abubuwa masu yawa. Ban da godiya da fatan alheri daga wajen 'yan uwa da ta taimakawa, abu mafi muhimmanci shi ne, kyakkyawar dangantaka a tsakanin mutane dake al'umma, baya ga daraja da ta samawa kanta

“A kan ce, muna taimakawa wasu ne, amma a zahiri mu na yiwa kanmu ne. A lokacin da muke yin kyawawan ayyuka, ma kan yi farin ciki, kuma a ganinmu, muna da amfani.”

Mahinur tana ganin cewa, cikakken tsari da kokarin daidaita abubuwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Sin da ofisoshin jakadanci da kananan ofisoshin jakadancin da ke kasashen waje suke yi, sun samar da wata kafar kiyaye tsaro ga duk dan kasar da ya gamu da matsaloli a kasashen ketare, kuma sun sanya masu sa kai dake taimakawa ofisoshin jakadancin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, kana sun samar musu wani muhimmin dandamali don taka rawarsu a wannan fanni.

“Idan har babu taimakon gwamnati, hakika mu kadai, ba za mu iya yin abubuwa yadda ya kamata ba, ko kuma zai yi wahala mu gudanar da ayyukan ta hanyar samun tabbaci bisa cikakken tsari. Ina kuma godiya ga ofishin jakadancin da ya samar mana irin wannan dandamali, ta hanyar amfani da kwarewar mu, har mu zama masu taimakawa wasu.”

Mahinur ta bayyana cewa, a kwanan baya, a bisa jagorancin ofishin jakadancin, an kafa kungiyar ‘yan asalin kasar Sin dake kasashen waje dake Antalya. Kasancewarta shugabar kungiyar, tana kuma tunanin yadda za ta hada aikin kungiyar da aikin sa kai don kara wa Sinawa dake wurin kwarin gwiwar taimakawa ‘yan uwa da ke bukatar taimako.

“Burin mu shi ne, kafa kungiyar taimakawa juna tsakanin Sinawa, wadanda suka hada da ‘yan uwanmu, musamman wadanda suka kware a yaren wurin, dokoki, da kuma ayyukan gwamnatin kasar ta Turkiya. Idan Sinawa sun gamu da matsala, to, za a tallafa musu ba tare da bata lokaci ba.”