Kakakin Sin: Jama’ar kasa suke da ikon ba da maki kan hakkin bil Adama na kasarsu
2021-03-01 20:54:24 CRI
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin ta yi bakin ciki da takaici, kan yadda babbar kwamishina mai kula da aikin kare hakkin dan Adam ta MDD ta soki kasar, bisa wasu bayanai marasa tushe, da ma yadda wasu kasashe suka yiwa mata da kwamitinta matsin lamba.
Wang ya ce, jama’ar kasa, ba wai wasu daban ba, suke da cikakken ikon ba da maki, kan yanayin kare hakkin bal Adama a kasar su.
A daya bangaren kuma, game da yadda wasu kwararru masu sa iko kan aikin kare hakkin dan Adam na MDD suka nuna damuwa kan yadda ’yan sandan kasar Amurka suke amfani da karfin tuwo fiye da kima, Wang Wenbin ya ce, kasar Sin na fatan ganin Amurka ta dauki kwararan matakai na kare hakkin bil Adama. (Bello Wang)