logo

HAUSA

Sin: Wasu kasashen yamma suna keta aikin kare hakkin bil Adama a duniya

2021-02-26 20:11:55 CRI

Wasu kasashen yamma sun zargi kasar Sin a taron hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD ba tare da nuna sharidu ba, a don haka yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba shiryawa a nan birnin Beijing, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, wadannan kasashen yamma, sun saba siyasantar da batun hakkin bil Adama, kuma sun saba tsoma baki a harkokin cikin gida na sauran kasashe, duk wadannan sun kawo tarnaki ga hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a fannin kare hakkin bil Adama, kuma hakan keta babban aikin kare hakkin bil Adama ne a duniya.

Wang ya kara da cewa, kasar Sin tana yin adawa da wasu kasashe ko hukumomi saboda sun yi watsi da hakikanin abubuwa, sun baza jita-jita dake shafar yankunan Xinjiang da Tibet da Hong Kong na kasar Sin, domin shafawa kasar Sin bakin fenti.

Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin ta samu cikakkiyar nasarar yaki da talauci, har ta yi abin al’ajabi wajen kawar da talauci a tarihin bil Adama, wannan shi ma sakamako ne mai ma’ana a tarihi da kasar Sin ta samu wajen kare hakkin bil Adama, wanda ke taka babbar rawa kan ci gaban aikin kare hakkin bil Adama na duniya, kana sakamakon da kasar Sin ta samu, ya mayar da martani mai karfi ga zargin da wasu kasashe kalilan suke yi mata kan yanayin kare hakkin bil Adama da take ciki.(Jamila)