logo

HAUSA

Sin: Sin da Amurka sun fara tattaunawa kan batun sauyin yanayi

2021-02-26 20:13:05 CRI

Yau yayin taron ganawa da manema labarai, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya gaskanta cewa, manzon musamman na kasar Sin kan batun sauyin yanayi Xie Zhenhua da manzon musamman na shugaban kasar Amurka kan batun sauyin yanayi John Kerry sun fara tuntubar juna domin yin tattaunawa tsakaninsu.

Wang ya ce, nada Xie Zhenhua mukamin manzon musamman kan batun sauyin yanayi na kasar Sin ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali matuka kan batun matsalar sauyin yanayi, kuma kasar Sin tana son hada kai tare da Amurka da sauran kasashen duniya, domin kara karfafa aikin dakile sauyin yanayi, tare kuma da tabbatar da aiwatarwar yarjejemiyar Paris yadda ya kamata, kuma a karshe za a cimma burin samun ci gaban duniya ba tare da gurbata muhalli ba.(Jamila)