logo

HAUSA

Najeriya za ta horas da ma’aikatan lafiya da za su aiwatar da shirin rigakafin COVID-19

2021-02-26 20:18:51 CRI

Hukumomin lafiya a Najeriya, sun tsara wani shirin na samun horo ga ma’aikatan lafiyar da za su shiga shirin yiwa ‘yan kasar alluran rigakafin COVID-19 a matakan kasa da jihohin kasar, gabanin isowar alluran cikin kasar.

Da yake yiwa taron manema labarai karin haske kan shirin a Abuja, fadar mulkin Najeriya, shugaban hukumar lafiya a matakin farko ta kasar Faisal Shu’aib, ya bayyana cewa, ana horas da akalla ma’aikatan lafiya 13,000 a kashin farko na shirin.

Jami’in ya ce, shirin ya kunshi mahalarta daga matakan kasa da jihohin kasa, da kuma kananan hukumomi. Yana mai cewa, nan da ranar 1 ga watan Maris na wannan shekara, za a fadada shirin zuwa yankunan mazuba da wuraren taron jama’a, inda ake sa ran horas da ma’aikatan lafiya sama da 100,000

Manufar shirin a cewarsa, ita ce kara kwarewar ma’aikatan lafiya, wajen kula, da adanawa da bayar da alluran rigakafin gabanin isowarsu.(Ibrahim)