logo

HAUSA

Kasashen Sin da Habasha sun amince da bunkasa hadin gwiwarsu a bangaren fasaha

2021-02-26 10:31:34 CRI

Kasashen Sin da Habasha sun amince da bunkasa hadin gwiwarsu a bangaren fasaha_fororder_0226-Habasha-Faeza-hoto

Ofishin jakadancin Sin dake Habasha, ya ce kasashen biyu sun amince da bunkasa hadin gwiwarsu a bangaren fasaha.

An cimma yarjejeniyar bunkasa hadin gwiwa ce a ranar Laraba, yayin wata tattaunawa da ta gudana tsakanin Jakadan kasar Sin a Habasha, Zhao Zhiyuan da ministan kula da kirkire-kirkire da fasaha na kasar Abraham Belay.

Jami’an biyu sun tattauna kan hadin gwiwar kasashensu a fanin fasahohin sararin samaniya da maganin gargajiya da kafa yankunan masana’antu da cinikayya ta intanet da kuma rukunin gidaje na zamani.

A cewar Zhao Zhiyuan, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakaninsu shekaru 50 da suka gabata, Sin da Habasha sun shaida ganin karuwar musaya akai-akai a tsakaninsu, da kuma ingancin aminci a bangaren siyasa.

A nasa bangaren, Abraham Belay, ya godewa Sin bisa taimakon da take ba Habasha a bangarori daban-daban, musamman taimakonta a bangaren shimfida tubulin harbar tauraron dan adam na farko zuwa sararin samaniya. Ya kuma yi fatan kara karfafa hadin gwiwa da musaya a bangarorin da suka dace tsakanin kasashen biyu. (Fa’iza Mustapha)