logo

HAUSA

Yan bindiga sun sace dalibai a yankin arewa maso yammacin Najeriya

2021-02-26 20:21:38 CRI

Rahotanno daga Najeriya na cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da daliban makarantar sakandaren mata ta gwamnatin dake garin Jangebe a karamar hukumar Talata Mafara dake jihar Zamfara a yankin arewa maso yammacin kasar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Zamfara Abubakar Dauran, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema kabarai a Gusau, babban birnin jihar. Yana mai cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin ne da misalin karfe 2 na safiyar yau Jumma’a, inda suka yi awon gaba da daliban.(Ibrahim)