logo

HAUSA

UNICEF ya yi tir da yadda ake kara kai hare-hare kan dalibai a Najeriya

2021-02-26 20:44:13 CRI

Wakilin asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) a Najeriya Peter Hawkins, ya bayyana damuwa da ma yin Allah wadai da kakkausar murya, kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare kan dalibai a Najeriya

Peter Hawkins wanda ya bayyana haka cikin wata sanarwa, ya ce, asusun na UNICEF, ya bayyana takaici da bacin rai, kan yadda aka sake kai wani mummunan hari kan daliban makaranta a Najeriya. Yana mai cewa, asusun ya yi Allah wadai da harin, tare da yin kira ga wadanda ke da hannu da su gaggauta sakin yara matan, kana gwamnati ta dauki matakan tabbatar da ganin an saki yaran lami lafiya, da ma tsaron dukkan dalibai dake Najeriya.(Ibrahim)