logo

HAUSA

Masanin Rasha:Yadda tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa ya aza ingantaccen tushe ga cimma nasarar yaki da talauci

2021-02-26 14:09:09 CRI

Masanin Rasha:Yadda tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa ya aza ingantaccen tushe ga cimma nasarar yaki da talauci_fororder_微信图片_20210226141521

A gun taron jinjinawa wadanda suka ba da babbar gudummawa, wajen kawar da talauci a kasar Sin da ya gudana a jiya Alhamis a birnin Beijing, hedkwatar kasar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasarsa ta cimma cikakkiyar nasarar kawar da talauci.

A game da wannan, shugaban cibiyar nazarin harkokin gabas mai nisa karkashin kwalejin nazarin kimiyya na kasar Rasha, Alexey Maslov ya bayyana cewa, yadda tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa ba tare da tsayawa ba cikin shekaru sama da 40 da suka wuce, ya aza ingantaccen tushe ga cimma nasarar yaki da talauci.

A yayin tattaunawarmu da shi, Mr. Alexey Maslov ya yi nuni da cewa, duk da mummunan tasiri da annobar Covid-19 ke haifarwa, kasar Sin ta cimma burin da ta tsai da, na fitar da dukkanin al’ummu masu fama da talauci a kasar daga kangin da suka sami kansu a ciki, kafin karshen shekarar 2020 da ta gabata, kuma fasahohin kasar Sin sun cancanci sauran kasashen duniya su yi koyi da su. Ya ce,“Babu shakka, wannan gaggarumar nasara ce ga kasar Sin, da ma duniya baki daya. A karon farko a tarihin dan Adam, jama’a masu yawa irin haka suka fita daga kangin talauci a lokaci guda. Fasahohi da dabaru da kasar Sin ta aiwatar wajen saukaka fatara sun cancanci kasashen Afirka, da na Latin Amurka, da dai sauransu su yi nazari, kuma su yi koyi da su.”

Masanin Rasha:Yadda tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa ya aza ingantaccen tushe ga cimma nasarar yaki da talauci_fororder_微信图片_20210226141531

Mr. Alexey Maslov ya bayyana cewa, tun bayan da ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa da sauri cikin shekaru sama da 40 da suka wuce, lamarin da ya aza harsashi mai inganci ga kyautatuwar rayuwar al’umma. Ya kuma jaddada cewa, abin lura shi ne, kasar Sin ta aiwatar da aikin saukaka fatara ne sannu a hankali, a maimakon ta aiwatar da shi a dukkanin sassan kasar a lokaci guda. Yana mai cewa,“Manufar da kasar Sin ta tsara a wannan fanni ta yi daidai, wato ta tabbatar da bunkasuwar yankuna masu fama da talauci sannu a hankali a maimakon a lokaci guda. Misali, ta fara ne da bunkasa yankunan kudu maso gabashin kasar da ke mashigin teku, sa’an nan ta habaka wannan aiki har zuwa tsakiyar kasar da ma sassan yammacinta, matakin da ke da matukar muhimmanci wajen tabbatar da nasarar aikin.”

Masanin Rasha:Yadda tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa ya aza ingantaccen tushe ga cimma nasarar yaki da talauci_fororder_微信图片_20210226141527

A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, cikakkiyar nasarar da aka samu wajen kawar da talauci a kasar Sin, ta alamta babban ci gaban da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta samu, wajen hada kan al’ummar kasar, domin tabbatar da ganin rayuwar al’umma ta kyautata, kuma jama’ar kasar sun samu wadata.

Amma yadda aka samu nasarar kawar da talauci wani sabon mafari ne a maimakon a ce an zo karshen aikin. A game da zancen, Mr. Maslov ya ce, tuni kasar Sin ta tsara sabon burin da za ta cimmawa bayan da ta samu wannan nasara, ya ce,“A ganina, nasarar da kasar Sin ta samu wajen kawar da talauci, mataki ne na farko. Nan gaba, kasar za ta yi kokarin tabbatar da ganin alkaluman GDPn ta kan kowane dan kasar, ya kai matsakaicin matsayi na kasashe masu ci gaba, tare da kara kudin shigar al’ummar kasar baki daya, burin da za ta cimma nan da shekarar 2035. A ganina, kasar Sin ta tsai da inda za ta dosa, da ma burin da za ta cimma a nan gaba.” (Lubabatu Lei)