logo

HAUSA

Xi: Sin za ta aiwatar da matakan hade manufofin rage talauci da na raya karkara

2021-02-25 13:45:01 CRI

A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga sassan hukumomin kasar, da su zage damtse wajen aiwatar da matakan hade manufofin rage talauci da aka cimma a kasar da na raya karkara.

Shugaban na Sin, ya kuma bukaci da a ci gaba da mayar da batun magance matsalolin dake addabar fannin noma, da yankunan karkara, da manoma, a matsayin wadanda za a baiwa fifiko, cikin ayyukan da JKS ke gudanarwa.    (Saminu)

Saminu