logo

HAUSA

Sin: Matakin danne kamfanoni da gangan ba zai magance matsala ba

2021-02-25 21:34:08 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, ba zai yiwu ba a yi amfani da mataki na siyasa wajen sauya dokokin da suka shafi tattalin arzki, da danne wasu kamfanoni, kuma hakan ba shi ne zai magance matasala ba.

Rahotanni na cewa, a jiya ne shugaban Amurka Joe Biden ya sanya hannu kan wata dokar shugaba, domin sake bitar tsarin samar da wasu muhimman kayayyaki guda hudu, domin kawar da dogaro kan kamfanonin ketare dake samar da irin wadannan na’urori, musamman kamfanonin kasar Sin.

Da yake amsa tambayar da aka yi masa, Zhao Lijian, ya yi nuni da cewa, a wannan lokaci da duniya ke kara dunkulewa waje guda, muradun dukkan kasashen na kara hadewa waje guda. Kafawa da bunkasa tsarin samar da kayayyaki na duniya, sakamako ne kan matakan da aka dauka game da dokar da ta shafi kasuwa da zabin kamfanoni.(Ibrahim)