logo

HAUSA

Sin ta samu cikakkiyar nasarar yaki da talauci

2021-02-25 19:18:15 CRI

Sin ta samu cikakkiyar nasarar yaki da talauci_fororder_1

Yau Alhamis 25 ga wata, kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwa ta kasar sun kira babban taron yabawa wadanda suka ba da babbar gudunmawa wajen kawar da talauci a nan birnin Beijing, inda shugaban kwamitin kolin JKS kana shugaban kasar Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin ta samu cikakkiyar nasara wajen kawar da talauci bayan kokarin da daukacin al’ummun kasar suka yi a cikin shekaru takwas da suka gabata, bisa ma’auni na yanzu, manoman kauyukan fadin kasar kusan miliyan 100 wadanda suka taba fama da talauci sun fita daga kangin talauci daga duk fannoni, a sa’i daya kuma, ya jaddada cewa, akwai bukatar a ci gaba da yin kokari domin farfado da tattalin arzikin kauyuka, tare kuma da rage gibi dake tsakanin kauyuka da birane.

Tun farkon kaddamar da babban taron, shugaba Xi ya sanar da cewa,“Yau, mun kira wannan gagarumin taro domin sanar da cewa, mun samu cikakkiyar nasarar yaki da talauci, bayan kokarin da daukacin al’ummun kasar suka yi, bisa ma’auni na yanzu, gaba daya manoman kauyuka da yawansu ya kai miliyan 98 da dubu 990 sun fita daga kangin talauci, kuma an fitar da daukacin gundumomi 832 da kauyuka dubu 128 daga wadanda suke fama da talauci, kasar Sin ta cimma burin kawar da talauci a fadin kasar, ana iya cewa, ta yi wani abin al’ajabi a tarihin bil Adama.”

A cikin shekaru takwas da suka gabata, adadin mutanen da suka fita daga kangin talauci a kasar Sin a ko wace shekara ya kai miliyan 10, ba ma kawai kudin shigarsu ya karu ba, har ma rayuwarsu ita ma ta kyautata, shugaba Xi ya bayyana cewa, "Kudin shigarsu ya karu a bayyane, kuma suna samun isasshen abinci da sutura, kana an tabbatar da hakkinsu na samarwa ‘yayansu ilmi kyauta da inshurar jinya da gidajen kwana mai inganci.”

Hakazalika, fasahohin kawar da talauci na kasar Sin za su taka rawa kan aikin rage talauci a duniya, shugaba Xi yana mai cewa,“Muna nuna kwazo da himma domin gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya wajen rage talauci, kuma muna samar da tallafi ga kasashe masu tasowa, kasar Sin tana ba da gudummawarta ga yunkurin gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya.”

A karshe shugaba Xi ya bayyana cewa, nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakai domin tabbatar da sakamakon yaki da talauci da ta samu, tare kuma da ingiza farfadowar tattalin arzikin kauyukan kasar daga dukkan fannoni.”(Jamila)