logo

HAUSA

Makomar hadin gwiwar Sin da Amurka karkashin gwamnatin Biden

2021-02-24 09:18:49 CRI

A jajiberin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ne, shugabannin kasashen Sin da Amurka, suka zanta ta wayar ta tarho, matakin dake nuna makomarsu a nan gaba.

Makomar hadin gwiwar Sin da Amurka karkashin gwamnatin Biden_fororder_20210224世界21006-Sin da Amurka-hoto2

Yayin tattaunawar, shugabannin na Sin da Amurka wato, Xi Jinping da Joe Biden, sun cimma matsaya kan ingiza fahimtar juna da kawar da bambancin ra’ayi da kaucewa gaba da juna, da kara yin mu’amula da hadin gwiwa da juna.

Ban da haka, a matsayinsu na kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya, ya dace Sin da Amurka su gudanar da harkokinsu yadda ya kamata, su kuma hada kai don cimma muradun bil-Adama a duniya, saboda ganin barkewar cutar COVID-19 a duniya da koma bayan tattalin arzikin duniya da matsalar sauyin yanayi wadanda ba a taba gani ba a cikin tarihi.

Makomar hadin gwiwar Sin da Amurka karkashin gwamnatin Biden_fororder_20210224世界21006-Sin da Amurka-hoto3

A baya dangantakar kasashen biyu ta shiga wani mummunan yanayi, saboda yadda tsohuwar gwamnatin Amurka, ta rika daukar matakan da ba su dace ba kan kasar Sin, kamar tsamo baki a harkokinta na cikin gida, neman shafa mata bakin fenti, da take gaskiya, da sanyawa wasu kayayyakin kasar Sin haraji babu gaira babu dalili da makamantansu, don biyan bukatanta na siyasa, da yiwa tsarin siyasar kasar Sin gurguwar fahimta.

Masana na fatan sabuwar gwamnatin Amurka, za ta bullo da matakan da suka dace, na sake dawo da huldar dake tsakanin kasashen biyu kan turbar da ta dace. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)