logo

HAUSA

Shugaba Xi ya gana da wakilan masana da suka yi aikin kan tauraron dan Adam na Chang'e-5

2021-02-23 10:33:36 CRI

Shugaba Xi ya gana da wakilan masana da suka yi aikin kan tauraron dan Adam na Chang'e-5_fororder_20210223-saminu-Xi Jinping

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da wakilan masana kimiyya da injiniyoyi, da suka yi aikin bincike da kera tauraron dan Adam na Chang'e-5 na binciken duniyar wata.

Shugaba Xi wanda ya gana da masanan a babban dakin taruwar jama’a dake nan birnin Beijing a jiya Litinin, ya kuma kewaya wurin da aka ajiye samfura, wadanda bangaren na’urar tauraron na Chang'e-5 ya debo daga duniyar wata, da sauran abubuwa masu nuni ga nasarorin da Sin ta cimma a bangaren binciken sararin samaniya.

Da yake tsokaci game da hakan, shugaba Xi ya jinjinawa kwazon da aka nuna wajen cimma nasarar binciken duniyar wata, da amfani da damammakin sabon tsarin kasa na cin gajiyar albarkatu, da karfafa matsayin ilimin kimiyya da fasaha, da aiki tukuru don ciyar da kasa gaba.

Ya ce kamata ya ci gaba da aiwatar da manufofin raya binciken sararin samaniya sannu a hankali, a yayata sha’anin ci gaban kasar Sin ta fannin kirkire kirkire, tare da baiwa ci gaban bil Adama a wannan fanni gagarumar gudummawa. (Saminu Hassan)