logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kasa da kasa da su rungumi manufofin kare hakkin bil Adama masu sanya al’umma sama da komai

2021-02-23 10:31:15 CRI

Sin ta yi kira ga kasa da kasa da su rungumi manufofin kare hakkin bil Adama masu sanya al’umma sama da komai_fororder_210223-saminu-Wang Yi

Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan wajen kasar Wang Yi, ya yi kira ga kasashen duniya da su rungumi manufofin kare hakkin bil Adama, masu sanya al’umma sama da komai, tare da yayata akidun kare hakkin bil Adama na bai daya, da wadanda suke dacewa da wasu sassa kadai.

Wang Yi ya yi wannan kira ne ta kafar bidiyo a jiya Litinin, yayin taron manyan jami’ai na 46, na hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD ko UNHRC a takaice.

Ministan ya ce, Sin ta rungumi hanyar ci gaban kare hakkin bil Adama mafi dacewa da yanayin da take ciki, da kuma bukatun ta, shi ya sa a lokacin da aka samu barkewar cutar COVID-19, gwamnatin kasar ta bi salon kare rayukan al’umma gaban komai, ta yadda ba da kariya da tsaron rayukan daukacin al’ummar kasa ya kasance aiki mafi fifiko ga gwamnati, an kuma aiwatar da dukkanin matakai na cimma wannan buri.

Daga nan sai Wang ya tabo batun raba alluran rigakafin cutar COVID-19, wanda ya ce ya dace a gudanar da shi bisa adalci, kuma alluran su zama wadanda kowa zai samu cikin rahusa, ciki har da kasashe masu tasowa.

Game da jihar Xinjiang ta kasar Sin kuwa, Wang Yi ya ce ko alama, ba a taba samun wani yanayi na kisan kare dangi a jihar ba, kana ba wanda ke tilasawa al’ummun jihar yin wani aiki na tilas, ko hana al’umma ikon gudanar da addini, kana wadannan zarge-zarge, an kirkire su ne da mummunar manufa ta kiyayya.

Ya ce dokokin kasar Sin sun tanadi wanzar da tsaro a yankin Hong Kong, sun kuma haifar da sauyi game da yanayi na rashin tabbas da yankin ke ciki, tare da kare rayuka da ’yancin mazauna yankin na Hong Kong, ta yadda suke iya rayuwa karkashin tsarin doka mai nagarta.  (Saminu)