logo

HAUSA

Shugaban Zambia ya gana da babban jami’in diflomasiyyar Kasar Sin

2021-02-23 10:12:20 CRI

Shugaban Zambia Edgar Lungu, ya gana da babban jami’in diflomasiyyar kasar Sin, Yang Jiechi dake ziyara a kasar.

Yayin ganawar a jiya, Yang Jiechi, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, kuma daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin tsakiyar, ya mika sakon gaisuwa ta shugaban Sin Xi Jinping, ga shugaba Edgar Lungu.

Ya kara da cewa, Sin na mara baya ga Zambia a kokarinta na bin tafarkin ci gaba da ya dace da yanayinta. Ya ce bisa matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, Sin za ta karfafa musaya da Zambia a dukkan matakai, da zurfafa abotarsu da aminci, da hada hannu kan samar da dabarun ci gaba, da zurfafa hadin gwiwa wajen yaki da annobar COVID-19, da gina ababen more rayuwa da inganta zamantakewar al’umma.

Bugu da kari, Yang Jiechi ya ce a shirye Sin take, ta karfafa hada hannu da kasashen Afrika, ciki har da Zambia, wajen ingiza samun sabbin ci gaba a hadin gwiwarsu cikin sabon zamani.

A nasa bangaren, shugaba Edgar Lungu, ya ce yana mika sakon gaisuwar sabuwar shekara da fatan alkhairi ga shugaba Xi Jinping da al’ummar Sinawa, kana yana taya su murnar cika shekaru 100 da kafa JKS dake jagorantar al’ummar kasar zuwa ga manyan nasarori.

Ya ce Zambia na godiya ga Sin dangane da taimakon da ta dade tana ba ta. Kuma za ta nace ga kiyaye manufar Sin daya tak a duniya, sannan ta shirya hada hannu da Sin din wajen zurfafa hadin gwiwa domin amfanin al’ummominsu. (Fa’iza Mustapha)

Faeza