logo

HAUSA

Ana kara amfani da kudin Sin RMB a duniya

2021-02-22 10:54:11 CRI

Ana Kara Amfani Da Kudin Sin RMB A Duniya_fororder_人民币汇率

Alkaluman hadaddiyar kungiyar aikin sadarwa da hada-hadar kudi ta Worldwide Interbank ko SWIFT a takaice, sun nuna cewa, a watan Janairun bana, an kara yawan amfani da kudin Sin RMB a duniya, idan an kwatanta da sauran kudaden da ake amfani da su a duniya, inda har kudin RMB ya kai matsayi na 5.

Masana suna ganin cewa, an fara amfani da kudin RMB da kafar dama, lamarin da ya nuna cewa, an samu ci gaba wajen amfani da kudin na RMB a duniya, kana matsayin kudin ya rika samun kyautatuwa a tsarin kudaden kasa da kasa.

Wen Bin, babban manazarci a bankin Minsheng na kasar Sin ya yi nuni da cewa, muhimmin dalilin da ya sa ake kara amfani da kudin RMB a duniya a baya bayan nan shi ne, kasar Sin ta yi ta raya cinikin kasa da kasa a bara, kana kuma darajar kudin Sin RMB bai sauya sosai ba.

“A shekarar bara, kasar Sin ta yi ta raya cinikin kasa da kasa, inda yawan cinikin hajojin kasar Sin, da kuma rabon kasar Sin a kasuwannin duniya, dukkansu sun kai matsayin koli a duniya, lamarin da ya habaka bukatun kasa da kasa na amfani da kudin RMB. Sa’an nan kuma, tun daga shekarar bara, darajar kudin RMB ba ta sauya sosai ba. A bara, darajar kudin RMB ta karu da kaso 6.2 kan dalar Amurka. Lamarin da ya karfafa karfin zuciyar masu zuba jari na duniya kan kudin RMB.”

Rahotanni na cewa, a watan Yulin shekarar 2009, kasar Sin ta kaddamar da gwaje-gwaje kan biyan kudin RMB a tsakanin kasa da kasa, daga bisani, ta fadada gwaje-gwajen sannu a hankali. Yanzu haka yawan kudin RMB da ake biya a duniya, da rabonsa a duniya da kasar Sin take samu, yana karuwa a tsakanin kasa da kasa.

A ganin mista Wen, kara biyan kudin RMB a cinikin kasa da kasa ya nuna cewa, ana kara amfani da kudin RMB a duniya, kana kuma masu zuba jari na kasa da kasa, suna sa ran alheri kan makomar tattalin arzikin kasar Sin.

Bisa shawarar da aka gabatar kan shirin raya kasar Sin na shekaru biyar biyar karo na 14, an ce, nan da shekaru 5 masu zuwa, za a yi taka tsan-tsan kan kara azama, game da amfani da kudin RMB a duniya yadda ya kamata. Mista Wen ya yi bayani da cewa, yin amfani da kudin RMB a duniya zai dauki dogon lokaci, ba za a cimma burin cikin gajeren lokaci ba. Amma in an yi hangen nesa, to, akwai kyakkyawar makoma wajen kara amfani da kudin RMB a duniya. 

“Yanzu haka kasar Sin ta rika samun saurin ci gaban tattalin arziki. Kana kuma, tana fuskantar kyakkyawar makoma wajen raya tattalin arzikinta. Ban da haka kuma, darajar kudin Sin RMB ba ta sauya sosai ba, lamarin da ya samu amincewar kasa da kasa. Dukkansu suna taimakawa wajen kara azama kan kara amfani da kudin RMB a duniya. Har ila yau kuma, yanzu kasar Sin ta rika bude kofarta ga kasashen ketare, ciki had da kasuwannin hada-hadar kudi, da kara saukaka yin amfani da kudin RMB a fannonin cinikayya, da zuba jari da ajiya. Nan gaba, za a kara yin amfani da kudin RMB a harkokin ciniki, da a harkokin zuba jari, daga karshe, za a mayar da kudin na RMB a matsayin kudaden musaya. Kudin Sin na RMB zai kara yin tasiri a duniya. Baya ga haka kuma, a nan gaba, za a kirkiro karin hajojin hada hadar kudi da za a rika amfani da RMB wajen zuba jari a cikin su, lamarin da zai yi amfani wajen kyautata amfani da kudin a duniya.”

A sa’i daya kuma, ya zuwa yanzu ana fuskantar rashin tabbas, yayin da ake kara azama kan amfani da kudin RMB a duniya. Watakila za a sauya manufar dan sakin bakin aljihu a wasu kasashe, ta haka za a dakatar da zuba jari a kasashen da suka fi samun ci gaban tattalin arziki, kuma hakan zai samar da tangarda a kasuwannin hada-hadar kudi na duniya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan