logo

HAUSA

Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 3 a Najeriya

2021-02-22 20:42:58 CRI

Rahotanni daga Najeriya na cewa, an kashe ‘yan sanda uku, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan gidan ajiye namun daji na Ogba dake jihar Edo a yankin kudu masu gabashin kasar.

Da yake karin haske kan wannan lamari, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Moses Nkombe, ya bayyana cewa, babban darektan gidan namun dajin na Ogba, na daga cikin fararen hulan da ‘yan bindigan suka yi awon gaba da su a harin na ranar Lahadi.

Kakakin ya shaidawa manema labarai a Benin City, babban birnin jihar cewa, ‘yan sandan da aka kashe, suna gadin wurin ne, lokacin da aka kawo harin.

Nkombe ya ce, har yanzu babu wanda aka kama, amma ‘yan sanda suna gudanar da bincike. Haka kuma ana kokarin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.(Ibrahim)