logo

HAUSA

Xi ya gana da wakilan tawagar da suka harba Chang'e-5

2021-02-22 20:56:46 CRI

A yau ne, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da wakilan masana harkokin sama jannati da injiniyoyi da suka gudanar da bincike da aikin harba na’urar binciken duniyar wata ta Chang'e-5.

Xi ya jaddada cewa, ya kamata mu ci gaba da aikin da muka sanya a gaba, game da binciken sararin samaniya, da kara cimma sabbin sakamako a fannin kimiya da fasaha, da bude wani sabon babi sannu a hankali a fannin bincike, da ci gaba da bunkasa kirkire-kirkire a bangaren binciken sararin samaniya na kasar Sin, kana a kara ba da sabbi da gagarumar gudummawa ga yadda bil-Adama zai yi amfani da sararin samaniya cikin lumana.

Haka kuma, Xi ya ziyarci samfuran da na’urar Chang’e-5 ta dauko daga duniyar wata da aka baje, da ma nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin binciken duniyar wata.(Ibrahim)