logo

HAUSA

Shugaban Uganda ya gana da babban jami’in diflomasiyyar Sin domin kyautata dangantaka

2021-02-22 11:14:54 CRI

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya gana da babban jami’in diflomasiyyar kasar Sin Yang Jiechi wanda ya je ziyarar aiki a ranar Lahadi.

Yang, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, kana daraktan ofishin huldar harkokin kasashen waje na kwamitin tsakiyar JKS, ya gabatar da sakon fatan alheri na shugaba Xi Jinping zuwa ga Museveni, kana ya taya shi murnar sake yin nasarar lashe zaben shugaban kasar.

Yang ya ce sakamakon nuna kulawa da daga martaba daga shugabannin kasashen biyu keyi, dangantakar Sin da Uganda ta kafu bisa tafarki mai kyau. Kasar Sin tana cigaba da yunkurin lalibo hanyoyin bunkasuwa mafiya dacewa da yanayin kasa, kuma a shirye take ta yi aiki da kasar Uganda wajen kara zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da kyautata dabarun bunkasa cigaba, da fadada hakikanin hadin gwiwa karkashin shawarar ziri daya da hanya daya da kuma aiwatar da sakamakon da aka samu a taron kolin Beijing na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, da kuma daga matsayin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon mataki.

Museveni ya bukaci Yang da ya isar da sakon gaisuwar fatan alheri ga shugaba Xi Jinping, kana ya godewa kasar Sin bisa taimakon da take yiwa kasar da zuciya daya na ayyukan gina ababen more rayuwa, da bunkasa aikin noma da kokarin yaki da annoba a dogon lokaci, sannan ya yabawa muhimmiyar rawar da kasar Sin ke takawa wajen raya cigaban tattalin arzikin kasashen Afrika da kyautata yanayin zaman rayuwar al’ummar nahiyar.

Ya ce kasar Uganda tana dora muhimmanci kan dangantakar al’adu ta abokantaka a tsakanin Uganda da Sin, yana maraba da fadada zuba jarin da kasar Sin ke yi a kasarsa, kana ana fatan samun karin kayayyakin da zasu shiga kasuwannin kasar Sin, kuma a shirye take tayi aiki tare da Sin wajen gina shawarar ziri daya da hanya daya bisa ingantaccen tsari, domin samar da muhimmin cigaba karkashin hadin gwiwar dake tsakanin Uganda da Sin.(Ahmad)