logo

HAUSA

Kafar watsa labaran Amurka ta ce gwamnatin Amurka ta yada jita-jita kan Xinjiang

2021-02-22 20:47:42 CRI

Yau Litinin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, shafin yanar gizo na Grayzone na Amurka mai zaman kansa ya wallafa wani bayani, inda aka gaskanta cewa, tsokacin da aka yi wai “gwamnatin kasar Sin tana aiwatar da manufar kisan kare dangi kan ‘yan kananan kabilun yankin Xinjiang” karya ce, lamarin da ya nuna cewa, hakinanin abubuwan za su karyata jita-jita, kuma an san me ya faru a yankin.

Jami’in ya kara da cewa, yana fatan al’ummun kasa da kasa, za su fahimci ainihin yunkurin wadannan rukunoni masu adawa da kasar Sin, kada a amince da jita-jitar da aka baza, yana mai cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, masu hangen nesa da dama a fadin duniya suna kara gano yanayin da yankin Xinjiang na kasar Sin ke ciki, da manufofin da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa a yankin, a don haka, su kan nuna goyon bayansu a fili ga kasar Sin, ana sa ran nan gaba kafofin watsa labarai na kasashen ketare za su gabatar da rahotanni kan Xinjiang bisa adalci.(Jamila)