logo

HAUSA

Kafar watsa labaran Amurka: Amurka ta yi karya kan Xinjiang bisa rahoton karya

2021-02-21 17:31:56 CRI

A kwanakin baya ne wata kafar watsa labaran kasar Amurka ta bayyana cewa, gwamnatin Amurka ta zargi gwamnatin kasar Sin wai tana aiwatar da manufar kisan kare dangi a yankin Xinjiang bisa rahoton nazarin da wani mai tsattsauren ra’ayin addini ya gabatar, amma hakika wannan mai tsattsauren ra’ayin ya rubuta rahoton ne da alkaluman karya domin shafawa kasar Sin bakin fenti.

Shafin yanar gizo na Grayzone na Amurka, ya wallafa wani rahoton bincike a ranar 18 ga wata, inda aka yi nuni da cewa, gwamnatin Amurka da wasu manyan kafofin watsa labarai na kasashen yamma sun ruwaito wani rahoton nazari wanda wani mai tsattsauren ra’ayin addini Adrian Zenz ya wallafa a watan Yunin bara, inda suka zargi gwamnatin kasar Sin wai tana aiwatar da kisan kare dangi a yankin Xinjiang.

Rahoton shafin yanar gizon Grayzone ya yi nuni da cewa, a cikin rahotonsa, Adrian Zenz ya bayyana cewa, ana iya mayar da manufar kayyaden yawan al’umma a matsayin kisan kare dangi, saboda ya tarar cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, yawan wasu ‘yan kananan kabilun yankin Xinjiang ya ragu, amma alkaluman da ya ruwaito a cikin rahotonsa sun nuna cewa, yawan ‘yan kabilar Uygur dake yankin ya karu bisa babban mataki tsakanin shekarar 2010 zuwa ta 2018, kuma karuwar ‘yan kabilar Uygur a yankin ta fi karuwar ‘yan kabilar Han yawa tsakanin shekarar 2005 zuwa ta 2015, duk wadannan alkaluma ba su dace da ra’ayin da ya nuna ba.

Rahoton shafin yanar gizon Grayzone ya kara da cewa, wasu manyan kafofin watsa labaran kasashen yamma sun kira Adrian Zenz masanin harkokin kasar Sin, kuma sun kasa kula da ra’ayin da ya dauka kan siyasa da addini, hakika Adrian Zenz, ‘dan asalin Jamus ne mai tsattsauren ra’ayin addini, wanda ke aiki a asusun tunawa da wadanda suka sha wahalar kwaminis da gwamnatin Amurka ta kafa.(Jamila)