logo

HAUSA

Shugabannin G7 sun sanar da hada kansu wajen yaki da cutar COVID-19

2021-02-20 15:29:00 CRI

Shugabannin kungiyar G7, sun yi alkawarin hada hannu domin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 cikin hadin gwiwa, da kuma daukar 2021 a matsayin shekara ta musamman ta fuskar karfafa hadin gwiwa tsakanin sassa daban daban.

Shugabannin kungiyar G7 sun bayyana haka ne cikin sanarwar da suka fitar, bayan taron da suka yi ta kafar bidiyo a jiya.

Sun kuma yi alkawarin goyon bayan hukumar lafiya ta duniya WHO, don ta jagoranci duniya, a fannin gaggauta ayyukan nazari da raba allurar rigakafin cutar COVID-19, da karfafa ayyukan sarrafa allurar, da kara musayar bayanai tsakanin sassa daban daban, ta yadda za a tabbatar da raba allurar rigakafin cutar COVID-19 cikin adalci. (Maryam)