logo

HAUSA

Ci gaban hira da Sulaiman Ja’afar Abdullahi

2021-02-16 14:43:18 CRI

Ci gaban hira da Sulaiman Ja’afar Abdullahi_fororder_AA

A cikin shirin Sin da Afirka na makon da ya gabata, Murtala Zhang ya zanta da Sulaiman Ja’afar Abdullahi, wani dalibi ne dan asalin garin Zaria a tarayyar Najeriya wanda a yanzu haka yake karatun ilimin zirga-zirgar jiragen kasa wato Transportation Engineering a turance a jami’ar Central South dake birnin Changsha na lardin Hunan a kudancin kasar Sin, inda ya bayyana dalilin da ya sa ya kuduri aniyar karo ilimi a kasar Sin, da yadda yake jin dadin karatu a birnin Changsha, saboda a ganinsa, mutanen China mutane ne masu son hulda da jama’a.

Ci gaban hira da Sulaiman Ja’afar Abdullahi_fororder_BB

A ci gaban hirarsu a wannan mako, Sulaiman Ja’afar Abdullahi ya bayyana ingancin karatun da yake yi a jami’ar Central South dake Changsha, da ci gaban kasar Sin a fannin kera jiragen kasa masu sauri gudu da ake kira Fuxing. Haka kuma ya ce, hadin-gwiwar Sin da Najeriya a fannin shimfida layin dogo yana da muhimmanci sosai wajen raya harkokin sufuri da bunkasa tattalin arziki gami da kyautata rayuwar al’umma a Najeriyar.

Sulaiman ya kuma yi kira ga daliban Najeriya dake karatu a kasar Sin, su himmatu wajen karo ilimi da zurfafa dankon zumunci tare da mutanen China. Har wa yau, a daidai lokacin da al’ummar kasar Sin suke murnar bikin bazara a yanzu haka, Sulaiman ya taya Sinawa murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyarsu.(Murtala Zhang)