logo

HAUSA

Sulaiman Ja’afar Abdullahi: Ina jin dadin karatu a Changsha!

2021-02-09 14:13:46 CRI

Sulaiman Ja’afar Abdullahi: Ina jin dadin karatu a Changsha!_fororder_微信图片_20210208161950

Sulaiman Ja’afar Abdullahi, wani dalibi ne dan asalin garin Zaria wanda a yanzu haka yake karatun ilimin zirga-zirgar jiragen kasa wato Transportation Engineering a turance a jami’ar Central South dake birnin Changsha na lardin Hunan a kudancin kasar Sin.

A zantawarsa da Murtala Zhang, Sulaiman Abdullahi ya yi bayani kan takaitaccen tarihinsa, da kuma dalilin da ya sa ya kuduri aniyar karo ilimi a kasar Sin. Ya ce, yana jin dadin karatu a birnin Changsha, saboda mutanen China mutane ne masu son hulda da jama’a.

Har wa yau, Sulaiman Abdullahi ya bayyana ra’ayinsa kan bambancin yanayin karatu na gida Najeriya da na kasar Sin.(Murtala Zhang)