logo

HAUSA

Masar ta fara yi wa jami’an lafiya alluran rigakafin COVID-19 na kamfanin Sinopharm

2021-01-25 09:40:17 CRI

Ma’aikatar lafiya ta kasar Masar, ta ce an fara yi wa jami’an lafiya alluran rigakafin COVID-19 na kamfanin Sinopharm, jiya Lahadi a wani asibiti na lardin Ismailia dake arewa maso gabashin kasar.

Ministar lafiya ta kasar, Hala Zayed ce ta sanar da kaddamar da gangamin fara rigakafin COVID-19 a kasar, yayin wani taron manema labarai a asibitin bada daukin gaggawa na Abu Khalifa dake Ismailia.

Ministar ta yi bayanin cewa, gwajin da aka yi, ya tabbatar da rigakafin na kamfanin Sinopharm na da aminci da matukar inganci wajen kandagarkin COVID-19, musamman kandagarkin alamomin cutar masu tsanani.

Ta kara da cewa, hukumar kula da ingancin magunguna ta Masar, ta yi rigakafin Sinopharm rajista. Tana mai cewa cikin kwanaki masu zuwa, za a yi wa sauran alluran rigakafin kasar Sin da na Birtaniya da Rsaha rejista. (Fa’iza Mustapha)