logo

HAUSA

Ya kamata hadin gwiwa ya ci gaba da zama jigon alakar Sin da Amurka

2021-01-25 20:14:48 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, a baya hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka, ya kasance muhimmin abin da ake ambato a alakar sassan biyu, a don haka, ya kamata a ci gaba da wannan al’ada a nan gaba kan alakar kasashen biyu.

Rahotanni na cewa, shugaban majalisar ‘yan kasuwan Amurka dake nan kasar Sin, Gregory Gilligan, ya bayyana a kwanakin baya cewa, kimanin kaso 70 cikin 100 na kamfanonin Amurka 1,000 dake karkashin majalisar ‘yan kasuwan Amurka dake kasar Sin, ba su da wani shiri na ficewa daga kasuwar kasar Sin.

Da ya ke mayar da martani kan irin wadannan rahotanni, Zhao Lijian ya bayyana cewa, ‘yan kasuwan Amurka, sun sha nuna cewa, suna da tabbaci game da makomar ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, sun kuma bayyana kudirinsu na ci gaba da gudanar da harkokinsu na kasuwanci a kasar Sin, tare da nuna adawa da sabanin dake tsakanin kasashen biyu masu karfin tattalin arziki. Kalaman Mr Giliggan ya sake tabbatar da cewa, tattalin arzikin Sin da Amurka, da ma alakar cinikayya ta moriyar juna ce. Kasashen Sin da Amurka suna da muradu iri daya gami da babbar dama ta yin hadin gwiwa.(Ibrahim)