logo

HAUSA

Turkiyya tana kokarin ceton mutanen da aka yi garkuwa da su a tekun Gulf of Guinea

2021-01-25 11:21:33 CRI

Kasar Turkiyya tana ci gaba da amfani da matakan diflomasiyya domin tabbatar da sakin jirgin ruwa mai dauke da Turkawa 15 wadanda aka yi garkuwa da su bayan da ‘yan fashin teku suka kaiwa jirgin ruwan mai dauke da tutar kasar Laberiya hari a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa kasar Afirka ta Kudu daga kasar Najeriya, kamar yadda ministan harkokin wajen Turkiyyan ya bayyana.

A halin yanzu, jirgin ruwan yana yankin tekun kasar Gabon kuma a ci gaba da tuntubar dukkan kasashen da suka dace domin tabbatar da sakin Turkawan da aka yi garkuwa da su, a cewar ministan harkokin wajen kasar Turkiyyan Mevlut Cavusoglu a gidan talabijin din kasar NTV.

Ya ce, jirgin ruwan da aka yi garkuwa da shi ba mallakin kamfanin kasar Turkiyya ba ne, amma ma’aikatan jirgin 19 ‘yan kasar Turkiyya ne.

Jirgin ruwan mai suna Mozart wasu gungun barayi ne suka afka masa a ranar Asabar a wajen dake da tazarar mil 180 daga gabar tekun Lagas dake Najeriya. ‘Yan fashin jirgin sun yi garkuwa da mutane 15, mutum guda dan asalin kasar Azerbaijan ne wanda aka ba da rahoton an kashe shi a lokacin kaddamar da harin.(Ahmad)

Ahmad Fagam