logo

HAUSA

Akwai Rashin Daidaito A Fannin Raba Rigakafin COVID-19

2021-01-25 15:57:10 CRI

Akwai Rashin Daidaito A Fannin Raba Rigakafin COVID-19_fororder_新冠疫苗

Yayin da ake shiga shekarar 2021, kuma aka fara aikin rigakafin cutar COVID-19 sannu a hankali a sassan kasashen duniya daban daban, al’ummun kasa da kasa na fatan ganin karshen yaduwar wannan annoba. To sai dai kuma a hannu guda, ana fuskantar wasu matsaloli game da batun aiwatar da rigakafi.

A ranar 18 ga watan nan, hukumar lafiya ta duniya WHO, ta gudanar da taron kwamitin kolin ta na 148 ta kafar bidiyo. Yayin taron, babban daraktan WHO Tedros Ghebreyesus, ya nuna damuwa game da yadda ake rarraba alluran rigakafin.

Wasu alkaluma da kamfanin Airfinity mai hedkwata a birnin Landan mai lura da yadda ake gwaji, da nazarin nau’o’in rigakafin ya fitar, sun nuna cewa, kaso 85% na jimillar rigakafi da kamfanin Pfizer ke samarwa, da jimillar wadanda kamfanin Modena ke sarrafawa, dukkanin su ana kai su ne kasashe masu karfin tattalin arziki.

Wasu rahotanni ma na cewa, ko da tsakanin kasashen yammacin Turai da suke da damar samun rigakafin, ana samun jinkirin aiwatar da rigakafin yadda ya kamata. A ranar 18 ga wata, hukumar lura da ayyukan likitanci ta kasar ta Norway bayyana cewa, an samu wasu tsofaffi 33 dake zaune a gidajen kula da tsaffi da suka rasu, bayan da aka yi musu rigakafin cutar ta COVID-19 wadda kamfanin Pfizer ya samar.

Har ila yau a dai wannan rana, jihar California ta Amurka ta yi gaggawar dakatar da alluran rigakafin kamfanin Modena 330,000, bayan da aka samu mutane da dama dake shiga wani yanayi na rashin lafiya, bayan karbar rigakafin, sama da abun da masana suka kayyade.

A baya bayan nan, hukumar WHO ta ce tana tantance wasu karin alluran rigakafin COVID-19 13, ciki hadda na kamfanonin Sin 2, kuma 3 na matsayi na 3 na gwaji, wadanda kuma mai yiwuwa a fara amfani da su a lokutan gaggawa.  (Saminu Alhassan)

Saminu Alhassan