logo

HAUSA

An samu sabbin wadanda suka harbu da COVID-19 117 a babban yankin Sin

2021-01-25 11:02:47 CRI

An samu sabbin wadanda suka harbu da COVID-19 117 a babban yankin Sin_fororder_1127019458_16114843663181n

Rahotanni daga hukumar lafiya ta kasar Sin, na cewa a jiya Lahadi an samu sabbin wadanda suka harbu da cutar numfashi ta COVID-19 124 a babban yankin kasar, cikin su 117 sun harbu da cutar ne a cikin gida, kana mutane 7 sun shigo da ita ne daga ketare.

Game da wadanda cutar ta harba a cikin gida, hukumar ta ce akwai mutane 67 da aka samu a Jilin, da 35 a Heilongjiang, da 11 Hebei, da mutane 3 a birnin Beijing, kana da mutum 1 a Shanghai, wanda aka ce ya sauka a Shanghai din ne daga wajen kasar.

Sai dai kuma hukumar lafiyar ta ce ba a samu rasuwar ko da mutum guda, sakamakon harbuwa da cutar ba.

Ya zuwa jiya Lahadi, jimillar wadanda cutar ta COVID-19 ta harba a kasar Sin ya kai 89,115, ciki hadda mutum 1,850 da har yanzu ke samun kulawar jami’an lafiya, kana cikin adadin akwai 109 dake cikin matsanancin yanayi.   (Saminu)

Saminu Alhassan