logo

HAUSA

Xi: Ya dace a yi takara mai adalci a maimakon zargin juna

2021-01-25 21:17:57 CRI

Yau Litinin da yamma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron tattaunawa na “jadawalin Davos” na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya ta kafar bidiyo, inda ya gabatar da wani jawabi na musamman.

Cikin jawabinsa, Xi ya jaddada cewa, ya dace a nace kan ra’ayin hadin gwiwa na moriyar juna, ta hanyar yin takara mai adalci domin tabbatar da hakkin ci gaban kasashe daban daban a fadin duniya, bai kamata a rika zargin juna ba.

Xi ya kara da cewa, a karni na 21 da muke ciki, ya kamata a ci gaba da nacewa kan manufar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, bisa la’akari da sauye-sauyen da duniya ke ciki, ta yadda za a cimma burin kyautata tsarin gudanar da harkokin duniya, ya ce, kasarsa za ta ci gaba da yin kokari domin amfanawa daukacin bil Adama, kuma za ta dauki hakikanin matakai domin taka rawarta wajen tabbatar da dauwamammen ci gaban bil Adama, kana ya ce, kamata ya yi a yi amfani da sakamakon kimiyya da fasaha a bangaren kyautata rayuwar bil Adama, a maimakon kayyade ko hana ci gaban sauran kasashe.

Shugaba Xi ya nanata cewa, kasar Sin tana aiwatar da manufar diplomasiyya ta ‘yancin kai, tana kuma yin zaman jituwa da sauran kasashen duniya.

Hakazalika, Xi ya bayyana cewa, ko a lokacin da ake dakile rikici yanzu, ko yayin da ake gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya, hada kai da hadin gwiwa tsakanin daukacin bil Adama shi ne abu mafi muhimmanci.(Jamila)