logo

HAUSA

Xi Jinping: ya kamata kasa da kasa su tattauna tare kan batutuwan duniya da makomarta

2021-01-25 21:21:20 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya wato DAVOS tare da yin muhimmin jawabi ta hanyar yanar gizo.

Xi Jinping ya jaddada cewa, ma’anar ra’ayin bangarori daban daban ita ce kasashen duniya su tattauna batutuwan duniya tare, kana su tsaida makomar duniya baki daya. Ba za a iya tinkarar kalubale na bai daya ba idan dan Adam yana ciki duniya da ake zaman ‘yan marina, nuna kiyayya da juna, babu abin da zai haifar sai babbar illa ga dan Adam. A don haka,, ya kamata kasa da kasa su martaba ka’idoji da manufofin da aka cimma daidaito don daidaita harkokin duniya, ba wata kasa ko wasu kasashe ne kawai za su rika bada umurni ba.

Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata a yi amfani da ka’idoji da tsari don daidaita dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da kin amincewa da mai karfi ke yaki da maras karfi, kana bai kamata a rika fakewa da ayyukan ra’ayin bangare daya da sunan ra’ayin bangarori daban daban ba. Ya kamata kowa ya martaba ka’idojin da aka tsayar. Ra’ayin bangarori daban daban ba ra’ayi ne na son rai ba. Tarihi da halin da ake ciki yanzu sun shaida cewa, idan aka bi hanyar nuna kiyayya da juna, kamar yakin cacar baki, ko yakin ciniki, ko yakin kimiyya da fasaha, babu shakka hakan zai kawo babbar illa ga moriyar kasa da kasa da jama’arsu a karshe. (Zainab)