logo

HAUSA

Yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a nahiyar Afrika ya zarce miliyan 3.42

2021-01-25 09:45:59 CRI

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Africa CDC, ta ce zuwa jiya Lahadi, yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a nahiyar ya kai 3,421,147.

A cewar alkaluman hukumar, yawan wadanda cutar ta yi ajalinsu ya tsaya kan mutum 84,694.

Ta kara da cewa, kawo yanzu, mutane 2,881,677 daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu, sun riga sun warke.

Yankin kudancin Afrika ne ya fi fama da cutar bisa la’akari da yawan wadanda aka tabbatar sun kamu, sai kuma yankin arewacin nahiyar dake bi masa baya.

Cibiyar ta Afrika CDC ta ce kasashen nahiyar da cutar ta fi addaba bisa yawan wadanda suka kamu, sun hada da Afrika ta Kudu da Morocco da Tunisia da Masar da Habasha. (Fa’iza Mustapha)